Sabon tsarin tantance ministoci | Siyasa | DW | 09.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabon tsarin tantance ministoci

Majalisar dattawan Najeriya ta fitar da sharudda masu tsauri wanda ta ce wajibi ne wadanda aka mika sunayensu gabanta domin zama ministoci su cika kafin ta tantance su.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki

To wannan dai sabon salo ne majalisar dattawan ta takwas ta bullo da shi wanda ya saba da wanda aka sani a baya, domin kuwa majalisar ta ce dole duk wanda za ta tantancen ya samu amincewa daga sanatoci biyu na shiyyar da ya fito, tare da nuna takardar bayyana kadarorin da ya mallaka. Ko me suka hango suka dauki wannan mataki? Sanata Dino Melaye shi ne shugaban kwamitin yada labaru na majalisar dattawan ta Najeriyar.

Tsohon gwamnan jihar Rivers kana daya daga cikin wadanda sunayensu ke gaban majalisa Rotimi Amaechi

Rotimi Amaechi tsohon gwamnan jihar Rivers, daya daga cikin wadanda sunansu ke gaban majalisa

"Dole ne sai wadannan mutanen sun bi dokokin da ke cikin tsarin mulki na kasa, kana akwai dokokinmu na majalisar dattawa da za'a yi amfani da su kafin a gama masu bincike. Abin da kawai muka ce shi ne wadanda suka taba rike mukammin sanata da majalisar wakilai ba za'a yi masu tambayoyi da yawa ba kamar yadda za'a yiwa saura."

Korafi dangane da wasu sunaye

Tuni dai al'ummar kasar suka fara maida murtani a kan sabon matakin musamman fuskantar korafe-korafe a kan wasu mutanen da shugaban Najeriyar ya zabo don a basu minister, wanda yafi bayyana a fili shine tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi da kuma Hajiya Amina Ibrahim da wakilan jihohi Kaduna da Gombe ke korafi a kan ta. To ko 'yan siyasar Najeriya na ganin wadannan sharudda a matsayin mafita? Honourable Yuusf Mai-unguwa daga Nasarawa Ngom jigo ne a jamiyyar APC.

Majalisar dokoki a Tarayyar Najeriya

Majalisar dokoki a Tarayyar Najeriya

Son kai ko ra'ayin siyasa

"Wannan dodo rido ne kawai irin na siyasa suka bullo da shi, ai abin da ake nema shi ne mutanen da aka bayar sun can-canta ko kuwa. Kuma batun wai a samu sanatoci da za su tabbatar da zaben wadanda za'a bai wa mukamin ministoci na tabbatar da za'a samu."

Da alamu dai za'a kai ruwa rana wajen tantance wadanda za'a ba mukaman ministocin, musamman sauyi a kan wadanda suka taba zama sanatoci da a lokutan baya majalisar kan daga musu kafa wajen tan-tance su.

Sauti da bidiyo akan labarin