Sabon tsarin takaita rikicin ′yan awaren Ukraine | Labarai | DW | 20.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon tsarin takaita rikicin 'yan awaren Ukraine

Shugaban kasar Ukraine ya fitar da wasu kudurori 14 wadanda ya ke amannar za su maido daidaito tsakanin 'yan kasa

A wannan juma'ar ce shugaban kasar Ukraine ya fitar da wani shirin samar da zaman lafiya wanda zai taimaka wajen rage rigingimun 'yan awaren da ke goyon bayan Rasha a yankin gabashin kasar, wanda kuma ke barazana ga cigaba da kasancewar kasar ta Ukraine a dunkule waje guda.

Wannan shiri wanda ke dauke da kudurori 14, ya biyo bayan tattaunawar da shugaba Petro Poroshenko ya yi har sau biyu da shugaba Vladimir Putin na Rasha, a tsukin sao'i 72, bisa la'akari da cewa babu matsayar da za a cimma matukar ba a sami tallafin shugaban na Rasha ba.

Tun a jiya alhamis, Poroshenko ya gana da shugabani da masu hannu da shunin yankin gabashin kasar domin samun goyon bayansu a wannan tsari da ya kaddamar, ta yadda zai yi tasiri wajen kawo karshen makonni goman da aka dauka ana rikicin da ya hallaka akalla mutane 365.

Wannan shiri ya tanadi yin afuwa ga wadanda suka tafka manyan laifuka, kuma zai tabbatar da cewa sojojin hayan Rasha da Ukraine sun ficce daga filin dagan salin-alin.

Shirin ya kuma tanadi kananan hukumomi su fara aiki, matakin da shugabanin 'yan awaren da suka yi ikirarin samun yancin cin gashin kai daga Kiev suka yi watsi da shi.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe