Sabon rikici a gabashin Jamhuriyar Demukiradiyyar Kongo | Labarai | DW | 22.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon rikici a gabashin Jamhuriyar Demukiradiyyar Kongo

Wani kazamin fada da ya barke tsakanin sojojin gwamnati da ´yan tawaye a gabashin kasar JDK ya tilasta dubban mutane tserewa daga yankin. Wani wakilin dakarun MDD a yankin ya fadawa kamfanin dilancin labarun Reuters cewa sama da mutane dubu 50 sun tsere daga gidajensu, yayin da wasu dubu biyu suka tsere zuwa cikin Uganda. Su dai ´yan tawayen dake karkashin jagoranci wani tsohon hafsan sojin kasar, na adawa da shirin wanzar da zaman lafiya wanda ya tanadi gudanar da zaben gama gari a fadin kasar ta Kongo a cikin watan afrilu.