Sabon kokarin ECOWAS na yin sulhu a Mali | Siyasa | DW | 22.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabon kokarin ECOWAS na yin sulhu a Mali

A ranar Alhamis din wannan makon, wata tawaga da za ta hada shugabannin kasashe biyar na ECOWAS za ta isa kasar Mali domin kokarin warware rikicin siyasar kasar.

Nigeria Abuja | ECOWAS-Treffen (Reuters/A. Sotunde)

Shugabannin kasashe biyar na ECOWAS za su kai ziyara Mali

Tawagar shugabannin dai da aka bayar da sanarwar za su isa birnin na Bamako a ranar Alhamis, ta kunshi da shugaban kasar Senegal Maky Sall da na Cote d'Ivoir Alassane Ouattara da na Ghana Nana Akuffo Ado da shugaban kungiyar ta ECOWAS kuma shugaban Nijar Issoufou Mahamadou da kuma Shugaba Muhammadu Buhari na Tarayyar Najeriya. A baya dai kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAo, ta tura wata tawaga da ba ta samu nasarar sulhunta wannan rikicin ba, sai dai kungiyar ba ta gaza ba ganin cewa a yanzu kasar ta Mali na bukatar a daidaita abubuwa da dama da ke da mahimmanci a cikinta.

Mali Imam Mahmoud Dicko | Forderung nach Rücktritt von Präsident Ibrahim Boubacar Keita in Bamako (Reuters/M. Rosier)

Al'ummar kasar Mali na zanga-zangar samun sabuwar gwamnati

Wannan lamari dai na kasar ta Mali ya janyo hankulan kowa, inda majalisar dokokin kungiyar ta ECOWAS ta soma zaman taronta a ranar Litinin da tattauna batun na Mali. Sai dai da yake magana kan wannan batu dan majalisar dokoki na ECOWAS Alhaji Boukari Sani Zilly ya yi hannunka mai sanda ne, yana mai cewa akwai bukatar ganin ana shirya zabuka na gaskiya a Afirka. Ana iya cewa dai lokaci ya yi da kungiyar ta ECOWAS za ta bai wa kanta cikakkiyar daraja, ta yadda al'ummomin kasashen kungiyar za su ringa kallonta da kima. Abun jira agani dai shi ne ko al'ummar kasar ta Mali za su saurari wadannan shugabannin kasashe na kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO, ganin cewa da dama daga cikinsu ba su ma gyara rigingimun da ke cikin kasashensu ba, abun da ya sa ake ganin masu zanga-zangar za su zura idanu domin ganin ko shugabannin za su kare muradin ita al'ummar ne ko kuma kokarin kubutar da kujerar abokinsu Shugaba Ibrahim Boubacar Keita.

Sauti da bidiyo akan labarin