Sabon harin bam a Potiskum | Labarai | DW | 11.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon harin bam a Potiskum

Rahotanni daga garin Potiskum na jihar Yobe da ke arewacin Najeriya na cewar tashin bam ya yi sanadin rasuwar mutane 4.

Wakilinmu da ke Bauchi Ado Adullahi Hazzad ya rawaito mana cewar wasu mata biyu ne ciki kuwa har da mai shekarun da ba su gaza 15 ba ne ke dauke da bama-baman da suka tashi.

Wasu shaidun gani da ido sun gayawa Ado Hazzad din cewar baya ga wanda suka rasu ciki kuwa har da 'yan kunar bakin waken, mutanen da suka tasamma 30 sun jikkata wasunsu ma na dauke da munana raunuka.

Wannan harin dai na zuwa ne kwana guda bayan da bam ya tashi da wasu 'yan kunar bakin wake a babban chaji ofis din Potiskum din da kuma wani a kasuwar Monday Market da ke Maidurin jihar Borno wadda ke makotaka da Yobe din.