Sabon Gangamin adawa a Togo | Labarai | DW | 03.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon Gangamin adawa a Togo

'Yan adawa sun gudanar da zanga zanga a birnin Lome, boren da ke zama na ukun irinsa cikin tsukin wannan mako, a cigaba da neman shugaba Faure Gnassingbe, ya yi murabus daga kujerar shugabanci.

Mutumin da ya mulki Togo na tsawon shekaru 15 Gnassinbe dai, ya yi alkawarin tattaunawa da kungiyoyin 'yan adawa a watan Nuwamban da ya gabata,  tattaunawar da har yanzu bai kaddamar ba makonni bayan alkawarin.

Masu shiga tsakani na yankin yammacin Afirka da suka hadar da shugaban Ghana  Nana Akufo-Addo  da takwaransa na Gini  Alpha Conde, sun sha kokarin ganin an bude wannan tattaunawar ta da ci tura kawo yanzu.

Tun a shekara ta 2005 ne da Gnassingbe ya dare kujerar shugabancin kasar ta Togo biyo bayan mutuwar mahaifinsa Janar Gnassingbe Eyadema, wanda ya mulki kasar tsawon shekaru 38.