Sabon fada ya barke a zirin Gaza | Labarai | DW | 19.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon fada ya barke a zirin Gaza

Sabon fada ya sake barkewa tsakanin bangarori dake adawa da juna a zirin Gaza,wanda hakan wani fatali ne da yarjejeniyar da aka cimmawa ranar lahadi.

Tunda safiyar yau ne dai fada ya barke tsakanin magoya bayan Hamas da kuma magoya bayan shugaba Mahmud Abbas,inda aka kashe wasu jamian tsaro biyu daga kungiyar Fatah hakazalika wani dan sanda na kungiyar Hamas shima ya rasa ransa a musayar wuta da akayi a bakin asibitin shifa dake birnin Gaza.

Fada tsakanin bangarorin biyu mafi muni tun shekaru fiye da goma,ya barke ne tun bayanda shugaba Mahmud Abbas yayi kiran gaggauta gudanar da zabe a yankin,batu da kasashen yammam sukayi maraba da shi,sai dai dan majalisa mai zaman kansa Mustafa Bargouti yace bai kamata kasasne yamma su goyi bayan wani bangare a kokarin samarda demokradiya mai dorewa a yankin.