Sabon faɗa ya barke a birnin Mogadishu | Labarai | DW | 31.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon faɗa ya barke a birnin Mogadishu

Sabon faɗa da ya ɓarke a birnin Mogadishu na ƙasar Somalia ya yi sanadiyar mutuwar mutane aƙalla 12 a ranar Lahadi,8 daga cikinsu yan gida ɗaya. Iyalan sun rasa rayukansu ne a lokacinda wata nakiya ta faɗa kan gidansu cikin faɗa tsakanin sojojin sa kai da dakarun ƙasar Habasha kusa da babban filin wasan ƙwallon kafa na birnin Mogadishu. Faɗa a birnin Mogadishu ya halaka mutane fiye da 1000 tun daga shekarar bara tare da wasu kuma 600,000 da suka tsere daga birnin. Shekara guda da ya wuce sojojin Habasha suka fara taimakawa gwamnatin Somalia suna masu korar shugabannin islama waɗanda suka samarda zaman lafiya a yankuna da dama na kudanci da tsakiyar Somalia.