1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya: Neman gamsassun bayanai

Zainab Mohammed Abubakar
November 15, 2018

Saudi Arabiya ta bukaci Turkiyya ta rattaba hannu a yarjejeniyar hadin gwiwa kan binciken kisan gillan dan jarida Jamal Khashoggi ta hanyar wulakanta gawarsa a ofinshin jakadancin kasar da ke birnin Istanbul.

https://p.dw.com/p/38J1z
Fall Khashoggi - Gedenkveranstaltung in Washington
Hoto: picture-alliance/AP/J.S. Applewhite

 

Ofishin mai shigar da kara a madadin gwamnatin Saudi Arabiya, ya mika rokon da suka kira na " 'yan uwantaka" domin samun hadin kan mahukuntan na Turkiyya wajen gabatar musu da sakamakon binciken kisan wulakanci.

Sai dai a martaninta Turkiyya ta ce har yanzu Riyadh bata bayar da gamsassun bayanai game da kisan Khashoggi ba. Ministan harkokin wajen kasar Mevlut Cavusoglu ya ce sun yaba da matakan Saudi Arabiya, sai dai har yanzu babu gamsassun bayanai daga bangarensu.

Mai shigar da kara na masarautar Saudiyya ya shaidar da cewar, yanzu haka jami'an kasar biyar na fuskatar hukuncin kisa dangane da zargin hannunsu a kisan JamalKashoggi, mutumin da aka daddatsa gawarsa kafin yiwuwar narkarwa a Istanbul.