Sabin hare haren Isra´ila a Jenine | Labarai | DW | 16.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabin hare haren Isra´ila a Jenine

Rundunar tsaron Isra´ila ta kai wani saban samame, a yankin Jenine na Palestinu, da nufin capko, wasu daga yan ta´adan, da ta ke nema, ruwa jallo.

An yi masanyar wuta, tsakanin sojojin Israela, da dakarun ƙungiyar Al AQsa, tun da sanhin sahiyar yau.

Kazalika, tsakanin daren jiya zuwa asubar yau, rundunar Israela ta kama wasu Palestinawa 15, da ta ke zargi suma, da aikata ta´adanci.

A ɓangaren yahudawa, mutane 2, sun ji raunuka a cikin arangamar.

Wannan saban rikici ,ya biwo bayan wani da ya fi sa muni, wanda ya wakana ranar talata da ta wuce, a Jericho, inda sojojin Isra´ila, su ka yi dura mikiya, cikin gidan kurkuku, su ka yi awan gaba da wasu pirsinoni.