Inganta yaki da ta'addanci a Sahel
November 13, 2019Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar bakuncin shugabannin kasashen Chadi da Nijar da kuma Mali a jiya Talata a fadar Elysee inda ya ce za a sake bayyana takamaiman aikin rundunar Barkhan ta sojojin Faransa a yankin Sahel da kuma karfafa ta.
A lokacin wannan haduwa dai shugabannin kasashen na Nijar da Mali da Chadi sun bayyana damuwarsu kan matsayin birnin Kidal wanda har ya zuwa yanzu gwamnatin Mali ba ta da iko a cikinsa, sannan sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda kasashen duniya suka kasa cika alkawarin da suka dauka na tallafawa kasashen na Sahel a yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda.
Sai dai Shugaba Macron ya sha alwashin yin kira ga kasashen da suka yi alkawari kan su mutunta shi, sannan ya bayyana cewa za a samu karin sojoji a yankin zuwa karshen wannan shekara ko kuma farkon shekara mai kamawa.