1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin hare haren Dakarun Amurka a garin Samarra,Iraki

Zainab A MohammadMarch 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bu7P

IRAKI

Dakarun Amurka dana Iraki sun kai wasu miyagun hare hare a arewacin Bagadaza da yammacin yau,harin daya hadar da jiragen yaki sama da 50,da dakaru sama da 1,500,domin karkade abunda suka kira yan taada dake marawa shugaban Alqaeda na Iraki Abu Musab al-Zarqawi baya.

Wannan somame da dakarun Amurkan suka kai ayau a garin Samarra, na mai zama na farkon irinsa mafi girma,tun bayan hambare gwamnatin Sadam Hussein a 2003.Dakarun Amurkan dai na zargin magoya bayan Alqaeda da samun mafaka a garin na samarra dake cikin duwatsu.

Majiyar jamian Irakin dai na nuni dacewa sun kai harin na yau ne bisa ga rahotan da suka samu na dauki ba dadi dake gudana a arewacin Irakin.

Hare haren na arewacin Iraki,wanda kazalika ya hadar da motocin yaki 200,yazo ne adai dai ranar da majalisar Irakin ta kaddamar da zamanta na farko tun bayan zabe a watan Disamban shekarar data gabata.