Sabbin hare-hare sun hallaka mutane da dama a Iraƙi
April 24, 2013Tahse-tashen hankula sun kai ga hallakar wasu mutane 15 waɗanda a ciki 14 jami'an tsaro ne da 'yan bindiga, a misayar wutar da ya afku tsakaninsu, a cewar hukumomi.
Artabu tsakanin tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga kusa da garin Hawijah ya hallaka mutane 27 tun a ranar talata abun da ya janyo ramuwar gayyar da ta ƙara hallaka wasu 27.
Wannan kisan ramuwar gayyar ce ake cigaba da yi har a yau laraba inda kawo yanzu jami'an tsaro tara da 'yan bindiga uku sun hallaka. Masu zanga-zanga a yankunan da 'yan Sunni ke da rinjaye sun ɗauki watanni hudu suna gudanar da jerin gwano suna kuma kira ga shugaban ƙasa Nuri al-maliki da yayi murabus suna kuma yin Allah Wadai da zargin cewa hukumomin, waɗanda mafi rinjaye 'yan shi'a ne na muzgunawa tsirarun al'ummomin 'yan sunni.
Kawo yanzu dai, waɗannan hare-haren da aka fara ranar talata shine mafi muni a cikin waɗanda ake dangantawa da zanga-zangar ta 'yan Sunni.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman