Sabbin alƙalluma na cutar Ebola a yankin yammancin Afirka | Labarai | DW | 13.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin alƙalluma na cutar Ebola a yankin yammancin Afirka

Ƙungiyar Lafiya ta duniya WHO ta ba da rahoton cewar mutane sama da dubu goma suka mutu da cutar Ebola a yankin yammanci Afirka.

Ƙungiyar wacce ta bayyana haka a cikin sakamakon da ta sanar na ƙarshe a kan cutar a ranar goma ga wannan wata,ta ce a cikin ƙasashen uku masu fama da cutar Wato Laberiya da Saliyo da kuma Gini,ta ce mutane sama da dubu 20 suka mutu da cutar yayin da dubu goma da cikinsu suka mutu.

Sannan kuma ta ce an samu ɓullar cutar a cikin wasu ƙasashe guda shidda inda mutane 15 suka cikka.Sai dai ta ce a makwannin biyu na baya baya nan, an samu koma baya cutar a Laberiya.