Sababbin 'yan wasa a gasar Bundesliga
A ranar 24 ga watan Agusta ne aka fara kakar Bundesliga ta bana kuma a wannan shekarar ma kamar kowacce, wasu kungiyoyin kwallon kafa ta Bundesliga din sun sayi sababbin 'yan wasa.
Axel Witsel
Alex Witsel dan shekaru 29 da haihuwa wanda ya fito daga kasar Beljiyam ya shiga rukunin 'yan kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund. Irin rawar da ya taka a gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha na daga cikin abin da ya sa Dortmund din ta sayo shi daga kungiyar TJ Quanjian ta China kan kudi euro miliyan 20.
Paulinho
Bayer Leverkusen ta kashe euro miliyan 18 da rabi wajen sayen Paulinho dan Brazil. Gabannin zuwansa Leverkusen, dan wasan mai shekaru 18 da haihuwa ya taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Vasco da Gama. Paulinho dan wasa ne da ke kokari wajen taka rawa iri-iri a filin wasa kamar yadda shugaban sashin wasanni na Leverkusen Rudi Völler ya bayyana.
Matheus Cunha
Cunha da yanzu haka ya ke kungiyar RB Leipzig ya fara baje kolin kwarewarsa bayan da ya ci wa kungiyar kwallo a karawar da suka yi da BK Häcken a watan Yulin da ya gabata. Dan wasan mai shekaru 19 ya amince ya yi wa Leipzig wasa ne bayan da suka saye shi kan kudi euro miliyan 15. A baya dai Cunha wanda dan kasar Brazil ne ya yi wasa a kulab din FC Sion da ke Switzerland.
Kasim Adams Nuhu
Kasim Adams Nuhu da yanzu haka ya fara wasa a kungiyar Hoffenheim dan wasa ne da ka iya zame wa 'yan wasan gaba na Bundesliga babban kalubale saboda kokarinsa na tsare gida. Dan shekaru 23 da ya fito daga Ghana ya amince ya kasance da Hoffenheim bayan da suka saye shi kan kudi euro miliyan 8.
Alassane Plea
Zuwan Plea Borussia Mönchengladbach ya sanya burinsu na neman dodon raga ya cika. Kungiyar ta ce tana fatan dan wasan zai ba mara da kunya. Gabannin zuwansa Mönchengladbach kan kudi euro miliyan 23, Plea mai shekaru 25 da haihuwa ya yi wasa a kungiyar kwallon kafa ta Nice da ke Faransa.
Pablo Maffeo
Ana daukar Pablo Maffeo a matsayin kwararren dan baya da ke wasa a gefe a nan Turai. Kungiyar kwallon kafa ta Stuttgart ta sayi dan wasan kan kudi euro miliyan 10. Dan shekaru 21 da haihuwa, dan wasan ya fito daga kasar Spain kuma ya samu horo a cibiyar horas da 'yan wasa ta Manchester City da ke Birtaniya. Gabannin zuwansa Stuttgart, Maffeo a yi wasa a FC Girona a kasarsu.
Wout Weghorst
Wout Weghorst da ya fara wasa tun ya na shekaru 18 da haihuwa ya taka rawar gani a wasanninsa na baya. Da asalin kasar Holland, Weghorst yanzu haka ya na tare da kungiyar Wolfsburg wadda ta saye shi kan kudi euro miliyan 10 da rabi. Kafin zuwansa Jamus, dan wasan ya taka leda a kungiyar kwallon kafa ta AZ Alkmaar a Holland inda ya zura kwallaye 18 a wasanni 31.
Davy Klaassen
Werder Bremen ta biya tsabar kudi euro miliyan 13 da rabi wajen sayen Davy Klaassen. Davy dai dan wasan tsakiya ne da a baya ya ke wasa a kungiyar Everton ta Birtaniya. kafin nan kuma dan wasan mai shekaru 25 da haihuwa ya yi wasa a kungiyar Ajax ta Holland.
Jean-Philippe Mateta
"Ya na da gudu sosai sannan idonsa na kan inda kwallo ya ke" inji kociyan kungiyar kwallon kafa ta Mainz Sandro Schwarz a tsokacin da ya yi kan sabon dan wasan kungiyar Jean-Philippe Mateta wanda ya fara yi wa kungiyar wasa a kakar bana da aka sayo shi daga kungiyar Lyon ta Faransa a kan kudi euro miliyan 8.