Saakashvili ya lashi takobin yakar rashawa a Ukraine | Labarai | DW | 13.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saakashvili ya lashi takobin yakar rashawa a Ukraine

Bayan iza keyarsa daga kasar a ranar Litinin, jagoran adawar Ukraine ya yi alkawarin cigaba da shirya gangamin adawa da gwamnati daga kasar Poland inda ya ke yanzu.

A wannan Litinin din ce aka iza keyar Mikheil Saakashvili dagaUkraine zuwa Poland, lokacin da wasu mutane dauke da makamai da fuskoki a rufe suka yi awon gaba da shi daga wurin cin abinci a birnin Kiev zuwa filin jiragen saman kasar.

A taron manema labaru da ya gudanar a birnin Warsaw Saakashvili ya ce an fitar da shi daga kasarsa ba tare da amincewarsa ba, wanda hakan ya sabawa dokar kasa da kasa.

" Duk abunda Poroshenko ya yi, ni cikakken siyasar Ukraine ne, ko shakka babu ni dan asalin Georgia ne, amman kuma dan siyasar Ukraine a aikace. Zan cigaba da zama dan siyasar kasar, tare da yaki da rasahawa har sai na samu nasarar kawar da cin hanci a Ukraine da Georgia".

Saakashvili ya kasance shugaban kasar Georgia daga 2004-13, ka na daga bisani shugaba Poroshenko na Ukraine da suke dasawa a baya, ya bashi babban mukami a Ukraine, kafin dangantakarsu ta yi tsami.