Saad Hariri ya shirya zuwa kasar Masar | Labarai | DW | 21.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saad Hariri ya shirya zuwa kasar Masar

Hariri zai je birnin na Alkahira kai tsaye daga birnin Paris bayan tattaunawa da mahukuntan birnin kan matsalar da siyasar kasarsa ke fiskanta.

Firaministan kasar Lebanon Saad Hariri ya shirya zuwa kasar Masar a wannan rana ta Talata, kwana guda kafin komawarsa gida da tuni aka shiga dakon dawowarsa bayan da makonni biyu da suka gabata ya ce ya sauka daga mukaminsa.

Tun ma dai a ranar Lahadi ne ta shafinsa na Twitter Harairi ya ce zai je Masar kuma ofishinsa da ke a birnin Beirut ya tabbatar da hakan. Zai je birnin na Alkahira kai tsaye daga birnin Paris inda ya je tun a ranar Asabar ya kuma tattauna da mahukuntan birnin kan matsalar da siyasar kasarsa ke fiskanta.

Shi dai Shugaba Michel Aoun bai amince da ajiye mukamin ba na Hariri ya na kuma dakon komawarsa gida. Hariri dan shekaru 47 zai hakarci bikin tunawa da ranar 'yanci da za a yi a goben Laraba a birnin na Beirut.