SiyasaAfirka
Rwanda: Gwajin allurar rigakafin Marburg
October 3, 2024Talla
Ministan lafiya na kasar Rwanda Yvan Butera ya ce likitoci na bakin kokari wajen dakile yaduwar cuta Marburg ta hanyar killace wadanda suka kamu da kuma lura da su.
Ya ce ma'aikatar lafiyar na gudanar da gwajin allurar rigakafi tare da tsananta bincike da bayar da magunguna ga marasa lafiya da suka kamu da cutar mai haddasa tsinkewar jini, cutar da ke kama da Ebola.
Ma'aikatar lafiyar na sa ido kan mutane 410 da suka yi huda da wadanda suka kamu da cutar.