1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwanda za ta sake bude iyakarta da Yuganda

January 28, 2022

Hukumomi a Ruwanda sun sanar da cewa za a sake bude iyakokin kasar da Yuganda bayan kwashe tsawon shekaru uku na takun saka da tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/46D4I
Angola Luanda Friedensabkommen zwischen Uganda und Ruanda
Hoto: Presidency Rwanda

Wannan sanarwar na zuwa ne bayan ganawar da dan shugaba Yoweri Museveni na Yuganda Laftanat Janar Muhoozi Kainerugaba ya yi da shugaba Paul Kagame a karshen makon da ya gabata. Ana dai ganin ci gaban da aka samu zai bada gagarumar gudunmawa wajen gaggauta dawowar cikakkiyar alaka tsakanin Ruwanda da Yuganda.

Tun a shekarar 2019, dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen biyu bayan da Ruwanda ta zargi Yuganda da goyon bayan 'yan tawayen da ke adawa da shugaba Kagame. Duk da kokarin da kasashen kasashen Angola da Kwango suka yi don sassata rikicin, hakarsu ba ta cimma ruwa ba, wanda ya tillastawa Yugandar yin tattaunawar sirri da makwabciyarta.