Ruwan sama ya kawo karshen wutar daji a Spain | Labarai | DW | 29.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ruwan sama ya kawo karshen wutar daji a Spain

Wutar daji akalla 200 da suka tashi a wasu yankuna da ke Yammacin kasar Spain, sun lakume a alla Eka 2000 a cewar hukumomin yankin kafin ruwan sama ya kasheta.

Tsawon mako guda aka yi ana neman shayo kan wutar dajin amma abun ya ci tura. Sai a wannan karo da ruwan saman yayi maganin matsalar a cewar wata sanarwa ta gwamnatin jihar Cantabrie, inda aka yi fama da wannan matsala. Sanarwar ta ce ya zuwa safiyar wannan rana ta Talata, babu wata wuta da ke ci cikin dazukan yankin.

Wutar dai ta lashe fiye da Eka 2000 masu mahimmancin gaske, ciki har da filayan shakatawa da dama a cewar Shugaban yankin na Cantabrie Miguel Angel Revilla, kuma har ya zuwa wannan Talatar mutanan 700 da ke ayyukan kashin wutar cikin su har da sojoji sun kasance a wurin.