1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwan kudi ga yan wasan Super Eagles

February 15, 2013

Bayan da yan kungiyar Super Eagles suka dauki kofin Afirka, muhawara ta barke game da wanda yafi dacewa da koyarda yan wasan Afrika: Turawa ne ko yan Afirka?

https://p.dw.com/p/17epV
Hoto: Getty Images

To daga cikin al'amuran da jaridun na Jamus suka maida hankali kansu a wannan mako game da nahiyar Afirka, har da nasarar da yan wasan Najeriya, wato yan kungiyar Super Eagles suka samu a karshen wasannin  kofin kasashen Afirka da aka kare a Afirka ta kudu, inda  suka koma gida da wannan kofi. Jaridar Die Welt tace  dama dai akan ce wai duk wanda yayi da kyau to kuwa zai ga da kyau. Yan wasan na Super Eagles da mai koyar dasu, Stephen Keshi, zasu dade kudi bai zama wata matsala a rayuwarsu ba. Bayan alkawari na lada mai yawa daga  shugaban kasar ta Najeriya, suma yan kasuwa da masu sha'awar Super Eagles sun yi alkawarin kudi mai tsoka ga yan wasan. Dan kasuwa Mike Adenuga yayi alkawarin Euro dubu 750, kuma yace daga yanzu, shi da kansa ne zai rika biyan albashin malamin kwallon kafa, Stephen Keshi, kamar yadda   shima dan kasuwa Aliko Dangote yayi alkawarin kusan Euro miliyan guda ga yan wasan.

Nasarar da yan wasan Najeriya suka samu ta tayar da muhawara a game da masu koyar da kwallon kafa da suka fi dacewa da nahiyar Afirka: yan Afrika ne ko kuwa turawa, ko ace yan kasashen ketare. Jaridar Tagesspiegel tace tun kafin a fara wasannin na Afirka, mai koyar da yan Najeriya, Stephen Keshi yayi korafin cewar  masu koyar da kwallon kafa turawa dake zuwa Afrika, suna yin haka ne saboda kudi mai yawa da ake basu, amma  gwanintarsu bata kai ta yan Afirka ba. To sai dai jaridar Tagesspiegel tace ana sane da cewar hukumomin kwallon kafa da dama na Afirka basu yarda da masu koyarwa yan Afirka ba, sun gwammace su kira turawa kan wannan aiki. A wasannin da aka kare a bana, kasashe tara masu koyar dasu  turawa ne ko yan Amerika ta kudu, yayin da kasashe bakwai ne kadai suke da masu koyar dasu yan Afirka. A karshe dai  amsar wannan tambaya ta tabbata, domin kuwa  kasar da dan Afirka yake koyarwa ce ta sami nasara.

Ita kuwa jaridar  Die Tageszeitung tayi  sharhi ne a game da  fyade da yan tawaye da sojojin gwamnati suke ci gaba da yiwa mata da kananan yara a kasar Congo. Cikin watan Nuwamba sojojin gwamnati dake tserewa daga hare-haren mayakan yan tawaye, suka aukawa dan karamin garin nan mai suna  Minova, inda suka rika yiwa mata da kananan yara fyade. Wadanda suka yi fama da wannan mummunan abu sun rasa  wata hukumar da zata taimakesu, ko inda zasu kai kukansu. Wani likita a asibitin garin yace shi kansa ya kidaya mata akalla 95 da  aka ji masu rauni ta hanyar fyade. Majalisar dinkin duniya tace ana ci gaba da binciken wannan matsala,  yayin da  sojojin rundunar kiyaye zaman lafiya ta majalisar, wato Monusco suke ci gabada sintiri a wannan dan karamin gari.

M23 Rebellen Goma Kongo Afrika
Yan tawayen kungiyar M23 a jamhuriyar Demokradiyar KongoHoto: dapd

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta tabo shirye-shiryen  zabe a kasar Kenya a watan Maris mai zuwa, inda tace a karon farko yan takara sun fuskanci juna a wata muhawara ta television. Lokacin muhawarar  yan takarar sun tattauna munanan tashin hankalin da ya faru lokacin zaben shugaban kasa na shekara ta 2007, inda akalla yan Kenya 1100 suka  rasa rayukansu. Jaridar tace ko da shike an kammala dukkanin shirye-shirye na farar shari'ar wadanda ake zarginsu da zama ummul'aba'isin wannan tashin hankali , wadanda za'a gurfanar dasu gaban kotun kasa da kasa a birnin Hague, amma  har yanzu babu wasu matakai da aka dauka domin ganin irin wannan abu bai sake aukuwa ba, a lokacin zaben na shugaban kasa da na yan majalisar dokoki da za'a yi makonni hudu masu zuwa.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar