Ruto: Za mu amince da matakin hukumar zabe | Labarai | DW | 17.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ruto: Za mu amince da matakin hukumar zabe

Yayin da lokaci ke karatowa na sake gudanar da zaben shugaban kasa a Kenya, mataimakin shugaban kasar William Ruto yace za su martaba duk matsayi da hukumar zaben za ta dauka

Mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto yace ba za su damu ba idan hukumar zaben kasar ta amince da bukatun yan adawa yayin da ake shirin sake gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 26 ga wannan watan.

A watan da ya gabata ne dai kotun koli ta soke zaben ta kuma bada umarnin a sake gudanar da wani sabon zabe bayan da dan takarar adawa raila Odinga ya kalubalanci sakamakon wanda ya baiwa shugaba Uhuru Kenyatta Nasara.

Odinga ya kuma sanar da janyewa daga zaben yana mai cewa hukumar zaben ta gaza cimma sharudan da hadakar jam'iyyun adawar suka gabatar.