Rumbun boye makamai ya tarwatse a Iraki
June 7, 2018Talla
Hukumomin tsaro da likitoci a Iraki sun tabbatar da mutuwar mutane 16 tare da wasu 32 da suka jikata bayan fashewar abubuwa a wurin adana makamai kusa da unguwar 'yan shi'a a birnin Sadr d ake wani yanki na Bagadaza babban birnin kasar Iraki.
Rahotannin jami'an lafiya na cewa fashewar ta shafi mata da kananan yara, wani jami'an tsaro ya sheda wa kamfanin dillancin labarun AFP cewa, fashewar baya rasa nasaba da yawan manyan makamai da 'yan bindiga ke boyewa a tungarsu.