1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fashewar makamai ya kashe mutane a Siriya

Abdul-raheem Hassan
August 12, 2018

Akalla fararen hula 39 sun mutu cikin har da kananan yara da dama a garin Sarmada da ke lardin Idlib, bayan da wani rumbun ajiye makamai da ya tarwatse.

https://p.dw.com/p/332Zm
Syrien | Weißhelme bei der Rettung von Zivilisten
Hoto: Getty Images/AFP/M. Al-Bakour

Kungiyar kare hakkin bil'a Adama ta Syrian Observatory for Human Rights ta ce ana ci gaba da tsamo gawarwakin mutane da ke makale a karkashin baraguzan gini. Rahotanni na cewar yawancin wadanda suka mutun na da alaka da mayakan kungiyar Tahrir al-Sham da ta yi alaka da kungiyar 'yan jihadin kasar Siriya a shekarun baya. Kawo yanzu dai ba a kai ga gano musabbabin tarwatsewar wurin adana makaman ba, sai dai a baya-baya nan dakarun gwamnatin Siriya sun zafafa kai hare-hare da bama-bamai a kudancin Idlib a wani mataki na kwashe yankunan a hannun 'yan awaren gwamnati.