Rudani a yaki da Boko Haram | Siyasa | DW | 27.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rudani a yaki da Boko Haram

Ana samun bayanai masu karo da juna tsakanin Gwamna Kashim Shettima da rundunar sojan Najeriya kan hakikanin wuraren da yanzu haka 'yan ta'adda ke iko da su a jihar Borno

Shi dai gwamnan jihar Borno Alhaji Kashim Shetima, ya shaidawa wata tawagar gwamnatin tarayyar Najeriya cewa har yanzu Kungiyar Boko Haram ne ke rike da kananan hukumomin Abadam da Mobbar da kuma wani bangare na karamar hukumar Marte.

Wannan furuci na gwamnan dai na nuna cewa har yanzu da sauran aiki a kokarin kakkabe mayakan Kungiyar Boko Haram, daga jihar Borno nan da karshen bana, kamar yadda gwamnatin tarayyar da hedkwatar tsaron Najeriya ta tabbatar.
Sai dai wannan furuci na gwamnan bai yi wa babban hafsan Sojojin Najeriya Janar Tukur Buratai dadi ba, inda ya fito ya musanta hakan tare da cewa, babu wani bangaren Najeriya da ke hannun mayakan Kungiyar.


Magangannun bangarorin biyu sun jefa da dama cikin rudani, saboda a zaton an wuce matakin da ake magana, in aka yi la’akkari da nasarorin da ake bayyanawa kan Kungiyar wace a baya ta fito ta musanta. Al’ummomin da ke wadan nan yankuna sun tabbatar da cewa, kananan hukumomin da dama ne, ke karkashin ikon ‘yan kungiyar kuma yanzu haka, su ke gudanar da su ba tare da fuskantar wata matsala ba.


Kamar yadda wadanda suka shaida wa tashar DW ta wayar tarho, tabbacin lallai Boko Haram na iko da wasu yankunan, amma bisa sharadin za'a sakaye sunan sa saboda dalilai na tsaro. Masharhanta dai kamar Abubakar Baba Abdullahi, na ganin wannan ce-ce-ku-ce tsakanin bangaroin biyu ba zai haifar da alheri a wannan yaki ba.

Yanzu haka kuma matakin rufe kasuwanni a jihohin Yobe da Borno ya jefa al’ummar cikin mummunan hali na rayuwa, inda da dama ke rasa abin sawa a bakin salati. Isa Mai Kati Gashua, daya daga cikin al’ummar yankin da abin ya shafa ne, ya wa wakilin DW Al-Amin Suleiman Muhammed karin bayani, inda ya nuna yadda lamarin ya kawo cikas ga rayuwarsu.

Yanzu haka kuma akwai zargin cin zarafin jama’a da Sojojin ke yi a wannan yankin, inda ake kame almajirai da ma malaman da ba su san hawaba balle sauka.
Masana dai na ganin irin wannan mataki na kunci da ake jefa al’ummar ka iya hana su taimakawa jami’an tsaro a wannan yaki, inda suka bukaci a sake tunani kan irin wadan nan matakai.

Sauti da bidiyo akan labarin