1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rousseff ta yi nasara a zaben Brazil

October 27, 2014

Ci gaba da samun koma bayan tattalin arziki da sukurkucewar harkokin gwamnati na zama manyan kalubale da ke gaban shugaba Rousseff a karo na biyu a shugabancin kasar.

https://p.dw.com/p/1DcWt
Dilma Rousseff bleibt brasilianische Präsidentin
Hoto: Reuters

Dilma Rousseff ta sake samun nasarar ci gaba da jagoran cin kasar ta Brazil bayan wata tazara mara nisa da ta bawa a bokin karawarta a zaben kasar da ta fiskanci babban kalubale.

Shugabar dai ta samu nasarar samun kashi 51.6 cikin dari na kuri'un da aka kada, abin da ya sanya ta yi nasarar kan abokin karawar ta Aecio Neves cikin sakamakon da ya fita.

Shugaba Roussef ta nemi hadin kan abokan adawa wajen tun karar matsalolin da suka dabaibaye kasar, da suka hadar da koma bayan tattalin arziki da sauye -sauye a harkkokin siyasar kasar da harkokin gudanarwar ayyukan gwamnati, wani lamari da ya jefa kasar cikin zanga-zangar nuna adawa da tsare-tsaren gwamnati a titunan kasar a shekarar bara.

A cewar shugaba Roussef tattaunawa ita ce aba ta farko da za ta ba wa fifiko cikin wa'adin na ta karo na biyu, sai dai abin jira a gani shi ne yadda bangaren adawar zai karbi wannan tayi na ta.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo