Rouhani: Iran na da ′yancin kare kanta | Siyasa | DW | 11.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rouhani: Iran na da 'yancin kare kanta

Shugaba Hassan Rouhani na kasar Iran, ya nunar da cewa ba za su bar Amirka ta ci galaba a kan al'ummar kasar ba a yayin jawabinsa ga dubban mutanen da suka halarci bikin cika shekaru 40 da juyin-juya halin kasar.

Jawabin Rouhani na zuwa ne a dai-dai lokacin da al'ummar kasar ta Iran ke fama da matsin tattalin arziki sakamakon hauhawar farashin kayayyakin abinci da na masarufi da kuma karancín magunguna a asibitoci.

A ranar 11 ga watan Febarairun 1979 ne, sojojin kasar suka sanar da janyewarsu daga bangaren gwamnati tare da bayyana cewa yanzu ba su da bangare, abin da ya janyo rugujewar gwamnatin Shah Mohammad Reza Pahlavi da ke zaman shugaba da ya kasance babban na hannun daman Amirka a yankin Gabas ta Tsakiya tare kuma da kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Yayin jawabin nasa, Shugaba Hassan Rouhani ya nunar da cewa dandazon al'ummar da suka fito domin halartar wannan biki na nuni da cewa takunkuman da aka kakabawa kasarsa ba su kai ga cimma nasara ba.

Rouhani ya kara da cewa al'ummar kasar za ta sha fama da matsalar tattalin arziki sakamakon takunkumin da Amirka ta kakaba mata, sai dai  za su shawo kan matsalar ta hanyar taimakon junansu. Shugaban Amirka Donald Trump dai ya fice daga yarjejeniyar nukiliya ta shekara ta 2015, da Iran din ta cimma da manyan kasashe masu fada aji a duniya shida, da suka hadar da Amirkan da Rasha da China da Birtaniya da Faransa da kuma Jamus, tare da sake kakabawa Tehran din takunkumai a shekara ta 2018 da ta gabata, abin kuma da ya shafi tattalin arzikin kasar da mahukuntanta ke cewa yaki ne na tatalin arziki.

Sauti da bidiyo akan labarin