Rohingya: Daga fita cikin zafin wuta sai fadawa cikin bakin ciki
Dubban darurwan 'yan Rohingya sun fice daga Myanmar izuwa Bangladesh don samun tsaro. Sai dai a tsallaken kogin da ake kira Naf, bala'in yunwa da takura na dakonsu. Sansanin 'yan gudun hijra ya dade da cika.
Rashin tabbas ya sa ta tsere
Wannan iyalan Rohingya an koro su ne daga kasarsu. Sun yi kwanaki kan hanya kuma dole su tsallaka kogin da ke kan iyakar Myanmar da Bangladesh don samun tsaron rayuwarsu. Manufarsu ita ce cimma sansanin 'yan gudun hijira da ke Cox's Bazar a kusa da iyakar kasashen. Duk abin da suka mallaka sun kulla shi a leda daya da kuma kwando.
Ba damar yin gaba.
A gefen kogin sojojin Bangladesh na hana su tsallakawa izuwa ga sansanin 'yan gudun hijira. Sama da musulman Rohingya 582.000 suka tsere daga Myanmar izuwa Bangladesh, daga karshen watan Augusta izuwa yanzu, a cewar hukumar UNHCR.
Yaudara a kan ruwa
Tafiyan kwale-kwale a dan karamin rata sai an caje su Euro 40, kwatankwacin Naira 1600, wanda mutane kalilan ke da kudin biya. Ana kuma yawan samun nitserwar kwale-kwalen. Mutane da yawa na saida rayuwarsu ne a yin jira.
Wurin tsayewa don jiran tsammani.
Wannan matar da 'ya'yanta sun yi nasara. Sun tsallake masifar baya, yanzu sun isa waje mai tsaro a Bangladesh. Bayan tafiya cikin ukuba, a yanzu suna wanke jikinsu a wata fadamar shinkafa, yayin da suke dakon a kammala takardun barinsu tsallakawa izuwa Palang Khali, wanda ke daga cikin sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya.
Ba su san makomarsu ba
Daga tsallakawa kan iyaka dole daruruwan 'yan gudun hijiran Rohingya su dakata don samun izinin wucewa. A mako guda hukumar UNHCR ta yi kiyasin mutane 15.000 suka shiga Bangladesh. Dukkansu na bukatar isa Cox's Bazar, in da ake da sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya.
Cunkosa kuma babu dakin kwana.
Dubbansu an koro su ne daga kasarsu, 'yan Rohingya an tara su wuri guda kuma babu koda wurin yin bahaya balle ruwan sha mai tsabta, an barsu cikin tabo babu ko filin kwanciya. Ko da sun isa sansanin 'yan gudun hijiran a yanzu ya cika ya batse. za dai ace wani bala'i ne, domin kungiyoyin agaji na kasa da kasa ba wani tallafi mai yawa za su iya bayarwa ba.
Gidajen da aka kona
Rikicin na jihar Rakhine da ke yammacin Myanmar, ya yi kamari ne bayan da 'yan tayawayen Rohingya suka kai hari wa jami'an tsaro. Inda sojojin suka maida martanin rashin imani. An hallaka daruruwan Rohingya an kona gidaje da gonakinsu kurmus. MDD ta bayyana lamarin da cewa aikata laifin yaki da kuma kisan kare dangi, don kawar da al'ummar musulman daga kasar ma biya addinin Buddha.
Suu Kyi 'yar rigima
Kasashen duniya dai na sukar Aung San Suu Kyi, wace ke rike da kyauat zaman lafiya ta Nobel. Ta yi kiran samun hadin kan kasa, amma kuma gwamnatin kasar ta ci gaba da daukar Rohingya a matsayin bakin haure. Kazalika karfin fada aji na shugaban sojojin kasar Min Aung Hlaing, ya sa ta kasa yin suka a bisa azabar da ake yi wa 'yan Rohingya.