1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Yukrain na daukan sabon salo

February 22, 2014

Shugaban Viktor Ianukovitch ya fice daga fadar mulkin kasar da ke Kiev, yayin da majalisa ta albarkancin kudirin sakin tsohuwar firamnista Yulia Timochenko.

https://p.dw.com/p/1BDox
Hoto: Reuters

Majalisar dokokin kasar Ukraine ta zabi Alexander Turtshinov a matsayin sabon kakakinta bayan da Volodymyr Rybak na kusa da shugaban kasa ya yi murabus. Sabon kakakin ya na da hulda ta kut-da-kut da tsohuwar Firaminista Yulia Timochenko, wadda majalisar ta kada kuri'a kan a saketa daga gidan fursuna.

'Yan majalisa na bangaren adawa sun nemi Shugaba Viktor Ianukovitch ya ajiye aiki, wannan daidai lokacin da shugaban ya fice daga fadar mulkin kasar zuwa yankin da yake da goyon baya. Kuma tun bayan sanar da cewa za a koma amfani da kundin tsarin na kafin shekara ta 2004 da ya takaita karfin shugaban kasa, 'yan adawa suka kara himma na ganin bayan shugaban.

Tun farko Shugaba Ianukovitch ya amince da kiran zabe kafin lokaci, amma masu zanga-zanga na kara azama. Kamfanin dillancin labaran AP ya ruwaito wata kakakin tsohuwar firamnista Yulia Timochenko tana cewa an sake ta daga gidan fursuna, wannan bayan kuri'ar da majalisar dokoki ta kada na yin haka.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe