Rikicin tsakanin magoya bayan Hamas da na Fatah | Labarai | DW | 08.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin tsakanin magoya bayan Hamas da na Fatah

A ƙalla mutane 3 su ka rasa rayuka, da dama su ka ji raunuka,sahiyar yau, a wata arangama da ta haɗa magoyan bayan jam´iyun Fatah, da na Hamas a zirin Gaza.

Shaidu sun bayyana cewar rikicin ya ɓarke, bayan da wasu magoyan bayan jam´iyar Hamas, mai riƙe da Gwamnati, su ka yi yunƙurin sace wani, daga sojoji masu kulla, da lahiyar shugaban rundunar tsaro ta ƙasa.

Hakan ya hadasa sace sacen mutane, daga sassan 2 , kamin a fara arangara.

Ɓangaren Hamas, yayi wasti da zargin da ake masa, na fara tsokanar faɗan.

Idan dai ba a manta ba, tun ranar 22 ga watan da ya gabata, hulɗoɗi tsakanin Fatah da Hamas su ka daɗa taɓarɓarewa, bayan fito na fito tsakanin magoyan bayan jam´iyun 2.

Tun zaɓen watan janairu da ya wuce, Hamas ta samu nasara girka gwamnati, a ƙasar Palestinu.

Magabatan jam´iyun 2, sun gudanar da tarrurruka, domin kwantar da hankullan magoya bayan su, saidai, har yanzu ba su cimma nasara ba.