Rikicin siyasar Togo na kara yin kamari | Siyasa | DW | 26.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin siyasar Togo na kara yin kamari

Wutar rikici tsakani gwamnatin kasar Togo da 'yan adawar kasar ta kasr na cigaba da ruruwa, batun da ya sanya kungiyoyi ma'aikata a kasar suka basu shawara zaman kan teburin sulhu don kawo karshen rikicin.

Kungiyoyin na ma'aikata guda hudu wadanda ke da karfin fada a ji sun bukaci 'yan adawa kan su samar da da kudiri wanda zai warware rikicin siyassa da ake fuskanta a kasar Togo. Nadou Lawson daya daga cikin jiga-jigai na kungiyar kwadagon kasar ya ce ''a matsayinmu na ma'aikata muna kira ga 'yan siyasar kasarmu na ko wane bangare sun sassanta saboda abin ya ishe mu. Mu ma'aikata mu ne ke cikin tsaka mai wuya''.

Yayin da 'yan kwadago ke wadannan kalamai, masana da dama na cigaba da bada shawara ta yin sulhu tsakanin bangaren na gwamnati da na 'yan adawa sai dai duk da cewa masu shiga tsakani. Tuni dai 'yan adawa suka nuna amincewa da tattaunawar kamar yadda Nathanael Olympio wanda shi ne madugun gamayyar kungiyar 'yan adawa na Togo ya shaidawa manema labarai.

DW ta nemi jin ta bakin bangaren jam'iyya mai mulki a ta kasar Togo amma hakan bai samu ba. Su dai 'yan adawan na neman shugaba Faure Gnassingbe ya sauka daga karagar mulki maimakon sake tsayawa takara sannan suna son yi gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin domin kayyade wa'adin shugabanci amma gwamnati ta ki mika kai ga wannan bukata.

Sauti da bidiyo akan labarin