Rikicin siyasar Masar na daukan sabon salo
August 11, 2013Talla
Akwai yiwuwar gwamnatin wucin gadin kasar Masar da ke samun goyon bayan rundunar soja, za ta fara aikin kawar da magoya bayan hambararren Shugaba Mohamed Mursi, wadanda suke zaman durshen tun lokacin da sojoji suka yi juyin mulki.
Wasu majiyoyin tsaro da kuma na gwamnati sun ce, mai yiwuwa da sanfin safiyar wannan Litinin jami'an tsaro za su yi dirar mikiya kan magoya bayan hambararen shugaban.
Kuma ana daukan matakan kaucewa zubar da jini, yayin fito-na-fita da ake saran zai wakana.
Masu zanga-zanga suna neman ganin an dawo da Shugaba Mursi kan madafun ikon kasar ta Masar, saboda juyin mulkin da sojoji suka yi wa zababben shugaban ya saba ka'ida.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi