1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasar kasar Kodivuwa ya ki ci ya ki cinyewa

October 19, 2006
https://p.dw.com/p/BufN

´Yan tawaye a Ivory Coast wato Kodivuwa sun yi fatali da kiran da kungiyar tarayyar Afirka AU ta yi na shugaba Laurent Gbagbo ya ci-gaba da jagorantar kasar da yaki ya daidaita har tsawon wata shekara guda. Shugabannin ´yan tawayen kungiyar New Forces sun yi suka ga karin wa´adin da cewa zai kawo cikas ga shirin samar da zaman lafiya. A na sa ran cewa a cikin mako mai zuwa za´a gabatarwa kwamitin sulhun MDD wannan shawara ta kungiyar AU don a amince da ita. AU ta kuma ba da shawarar fadada ikon FM Charles Konan Banny. A ranar 31 ga wannan wata aka shirya gudanar da zabe a kasar ta Kodivuwa, amma aka dage shi saboda ci-gaba da fada tsakanin kungiyoyin da ba sa ga maciji da juna a yankin dake hannun ´yan tawaye a arewacin kasar da wanda ke karkashin ikon gwamnati dake kudu.