Rikicin siyasa a Bahrain | Siyasa | DW | 28.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin siyasa a Bahrain

'Yan adawar Bahrain sun shiga yunƙurin ɗinke ɓaraka domin tunkarar gwamnati

ARCHIV - Der Herrscher von Bahrain, König Hamad bin Issa al-Chalifa, aufgenommen am 27.10.2008 im Schloss Bellevue in Berlin. Einen Tag nach der Verlegung von arabischen Truppen nach Bahrain hat sich die Lage in dem arabischen Königreich dramatisch zugespitzt. König Hamad bin Issa al-Chalifa verhängte am Dienstag (15.03.2011) für drei Monate den Ausnahmezustand. Nach Angaben aus Oppositionskreisen kam es in der Hauptstadt Manama und in der Ortschaft Sitra zu gewalttätigen Ausschreitungen zwischen Demonstranten und Angehörigen der Sicherheitskräfte. Foto: Gero Breloer dpa +++(c) dpa - Bildfunk+++ pixel

Sarki Hamad bin Issa al-Chalifa na Bahrain

Kimanin shekaru biyu kenan da fara zanga zangar nuna adawa da Gwamnati a ƙasar Bahrain dake yankin Tekun Fasha. An samu haɗin kai tsakanin ɓangarorin musulmi na Shi'a da sunna dake ƙasar a farkon zanga zangar inda suke kira da ayi gyara a tsarin mulkin masarautar ƙasar da Sarki Al-Khalifa ke jagoranta.To amma a baya bayan nan sai gashi an fara samun rarrabuwar kai a tsakanin ɓangarorin biyu.

Akwai mutane da dama dake goyon bayan gwamnatin ƙasar a farkon wannan zanga zanga, to amma daga baya sai suka koma ɓangaren masu zanga zanga.

Jihan Kazerooni na ɗaya daga cikin irin waɗannan mutane.Ta ce a lokacin da aka fara zanga zangar nuna adawa da mulkin masarautar ƙasar ta kasance ta na goyon bayan gwamnati kasancewar ba ta yi tsammanin akwai talakawa da masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar ba.

Kazerooni wadda ta kasance ma'aikaciyar banki inda ta ke zaune a wani katafaren gida tare da tuƙa mota mai tsada ta fito daga ɓangaren musulmi na Shi'a waɗanda ke goyon bayan wannan zanga zanga, saidai kasancewarta mai hali ya bada gagarumar gudunmawa wajen goyan bayan gwamnati maimakon ɓangaren Addini da ta fito.

Kazerooni ta ce: Na amince da abin da gidan talabijin na ƙasar Bahrain ke faɗa cewa masu zanga zangar na ɗauke da makamai kuma sannan su maƙaryata ne, harsai ranar da na halarci shataletalen Pearl inda na ga jami'an 'yansanda su na kai hari kan masu zanga zangar da basa ɗauke da makamai ,wanda hakan ya sanya idanuna su ka gaza runtsawa.

Kazerooni ta ce ta ga abubuwa da dama da ba zata manta ba a lokacin da ta halarci dandalin na Pearl da masu zanga zangar su ka yi dandazo domin ganewa idanunta gaskiyar abinda ke faruwa.

Bayan da ta dawo gida ta yanke shawarar kafa wani asusun haɗin gwiwa domin kare haƙƙin danadam inda ta kai ziyara ga shugaban cibiyar kare hakkin danadam na kasar ta Bahrain Nabil Rajab tare da yamowa mamba.

Kazerooni tace haryanzu tana tuna hadin kan da aka samu a farkon wannan zanga zangar tsakanin bangaren Shia da Sunna kafin daga bisani gwamnati tayi kokari matuka wajen raba kan yan kasar domin ta dakushe karfin yan adawa.Tayi nuni da wani kauye da bashi da nisa da Manama babban birnin kasar ta Bahrain inda tace Yan shia ke zaune a wannan kauye saidai suna fama da talauci da kuma rashin cigaba in aka danganta da birnin na Manama.

Atmo

Bada jimawa bane jamian yansanda suka kai farmaki gidan wani dan shia Abdallah Al Mizo da misalin karfe 3 na dare inda sukaci zarafinsa wanda hakanne yasanyashi zargin yansunna tare da kin amincewa dasu.

Ali Salman shine shugaban babbar kungiyar Adawa ta Al-Wefaq ya zargi masarautar da yin amfani da dabaru da kuma karfin mulki wajen janyo rashin yadda da aminci tsakanin ɓangarorin biyu.

Ya ƙara da cewa ida zarar an samu rarrabuwar kai da ƙyamar juna tsakanin ɓangaren shi'a da sunna, to fa ba wani zaɓi da ya wuce goyon bayan gwamnati.

A ɓangare guda kuma mai magana da yawun gwamnatin ta Bahrain wanda ya kasance danuwa ga Al-Khalifa wato Abdulaziz Khalifa ya musanta cewa gwamnati na ƙoƙarin raba kan ɓangarorin biyu.

Abdulaziz Al-khalifa ya ce: Ba ruwan gwamnati da wane ɓangare na Addini ke goyon bayan gwamnati da kuma wannene baya goyon bayan gwamnati. Matsalar dake akwai shine idan suka tashi bayyana ra'ayoyinsu a tsakaninsu sai ya koma matsalar siyasa da addini.

To koma dai me ya janyo rarrabuwar kan duka ɓangarorin biyu sun yarda cewa abin na ƙara ƙamari, saidai sabuwar mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam Jihan Kazerooni ta yi iya ƙoƙarinta wajen daƙile rarrabuwar kai tsakanin 'yan Shi'a da Sunna inda ta taimaka wajen kafa ƙungiyar wayar da kan 'yan ƙasar tare kuma da yaƙi da tashe tashen hankula mai suna BRAVO wadda ta maida hankali wajen wayar da kan waɗanda gwamnati ta azabtar da su wanda a ganinta hakan shine kaɗai mafita wajen kawo ƙarshen banbancin aƙida tare kuma da sake gina ƙasar ta Bahrain ba tare da wani banbanci ba.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Sauti da bidiyo akan labarin