1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sauke firaministan Sri Lanka daga mukaminsa

Zulaiha Abubakar MNA
October 27, 2018

Shugaban kasar Sri Lanka Maithripala Sirisena ya sallami firaministan kasar daga aiki bayan ya sanar da maye gurbinsa da Mahinda Rajapaksa wani na hannun daman Shugaba Sirisena.

https://p.dw.com/p/37GUD
Sri Lanka Präsident Maithripala Sirisena und Premierminister Ranil Wickramasinghe
Shugaban Sri Lanka Maithripala Sirisena da Firaminista Ranil WickramasingheHoto: Imago/Zumapress/T. Basnayaka

Tuni dai wannan canji ya fara haifar da yamutsi a siyasar kasar ta Sri Lanka sakamakon ikirarin da firaminista mai barin mulki ya yi na cewar shi ke da mafi rinjayen magoya baya a zauren majalisar dokokin kasar, don haka ba zai sauka daga mukaminsa ba.

A nasa bangaren sabon firaministan ya shaida wa manema labarai cewar ya shirya tsaf don fara gudanar da aiki tare da shugaban kasa Maithripala Sirisena.

Shi dai Shugaba Sirisena wanda ya dauki tsawon shekaru tara yana mulki bayan yakin basasar da ya faru a kasar, ana zarginsa da cin hanci da karbar rashawa da kuma cin zarafin 'yan jarida da gana musu azaba.