Rikicin nukleyar kasar Iran | Siyasa | DW | 21.02.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin nukleyar kasar Iran

An kammala ganawa tsakanin Iran da Rasha a game da rikicin nukleya

Jiya ne tawagogin kasashen 2, su ka fara wannan tantanawa, da zumar samar da bakin zare warware rikicin nukleya na kasar ta Iran.

Idan dai ba a manta ba,hukumar yaki da yaduwar makaman nuklea ta majalisar dinkin Dunia, bisa bukatar Amurika da kasashen kungiyar gammaya turai, ta yanke shawara gurfanar da Iran gaban komitin sulhu, bayan kiki kakar da aka huskanta a tarruruka daban daban da a ka gudanar na ciwo kan wannan matsala.

Jim kadan bayan yake shawara, gurfanar da ita, gaban komitin sulhun Majalisar Majalisar Dinkin Dunia, kasar Iran, ta bayyana ci gaba da shiyre shiryen ta, na sarrapa Uranium, da nufin samara da makamashin Nuklea.

Amurika da kungiyar gamaya turai, na tuhumar Iran da labewa ga guzuma domin harbin karsana, wato za ta anfani da sallon samar da makamashin nuklea, amma a fakaice, da kera makaman nuklea, abinda ke zama barazana ga kwanciyar hankali a dunia.

Don samun massalaha a cikin wannan takkadama, kasar Rasha, da ke goyan bayan Iran, ta yi wa hukumomin kasar tayin hakko hakka tashoshin samar da makamashin nukleyar, a Rasha, abinda kila, zai kau da duk wani zargi, da turai da Amurika ke mata.

Bayan yini 2 na masanyar ra´ayoyi a game da batun, shugaban tawagar kasar Iran, Ali Hossni-Tash ya bayana manema labarai cewa an samu babban ci gaba a cikin tantanawar.

Saidai kafofin sadarwa a kasar Rasha sun ruwaito cewa, ci gabanda a ka samu, irin na mai hakar rijiya ne.

A cewar jaridun Iran na bukatar anfani ne kawai ,da wannan dama domin jinkirta matakin gurfanar da ita, gaban komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia,da kuma sakamakon da zai biwo baya, na saka mata takunkumi ,ko kuma shiga kafar wando guda da Amurika.

Alamomin da ke nuna hakan, sun hada da kalamomin da sakataren harakokin waje, na kungiyar gamaya turai Havier Solana yayi, wanda bayan ganawar da yai jiya da ministan harakokion wajen Iran Manouchehr Mottaki, ya bayyana cewar, babu wani cenji da ka samu , har yanzu, Iran na tsaye a kan matsayin ta .

Kazalika, ministan harakokin wajen na Iran,bayan komawar sa gida Teheran, ya bayana cewar, Iran ta katse duk tantanawa a kan batun, da tawagar kungiyar gamayya, turai da ta hada da Jamus, France da Britaniya.

A nata gefe ,a yanzu haka, sakatariyar harakokin wajen Amurika, Condolesa Rice, na ci gaba da ziyara, a yankin gabas ta tsakiya, inda ta je domin samar da goyan baya, a kan mataka ladabtar da Iran.

A dangane da tantanawar kuma, tsakanin Iran da Rasha, tawagogin 2, za su ci gaba ranar alhamis idan Allah ya kai mu.

 • Kwanan wata 21.02.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu1Z
 • Kwanan wata 21.02.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu1Z