Rikicin Masar ya zafafa | Labarai | DW | 28.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Masar ya zafafa

Mutane uku sun hallaka yayin dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaron Masar da masu zanga-zanga.

Mutane uku sun hallaka yayin fito na fito tsakanin 'yan sandan kasar Masar da masu zanga-zangar da ke goyon bayan kungiyar 'Yan Uwa Musulmai, yayin da aka cafke fiye da mutane 260.

A wannan Jumma'a 'yan sandan sun yi dauki ba dadi da masu zanga-zanga a Alkahira babban birnin kasar, da gabashin birnin Nasr City da kuma wasu sassa na kasar. Sabon rikicin ya biyo bayan matakin mahukuntan na tsauraran matakai kan magoya bayan kungiyar 'yan uwa Musulmai, kungiyar da hukumomi suka aiyana a matsayin ta 'yan ta'adda.

Dalibai na cikin wadanda suka shiga cikin magu zanga-zangar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman