Rikicin Masar na daukan sabon salo | Labarai | DW | 28.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Masar na daukan sabon salo

Dalibi daya ya rasa ransa cikin artabu tsakanin jami'an tsaron kasar Masar da masu zanga-zangar.

Dalibi daya ya rasa ransa sannan an kama wasu kimanin 60, yayin fito na fito tsakanin jami'an tsaron kasar Masar, da dalibai da ke goyon bayan kungiyar 'yan uwa Musulmai, wadda mahukunta suka aiyana a matsayin ta 'yan ta'adda. Majiyoyin asibiti sun tabbatar da mutuwar, amma jami'an tsaro sun musanta.

Wasu rahotannin sun ce wasu gine-gine na jami'ar Al-Azhar da ke birnin Alkahira sun kama da wuta lokacin artabun. Kasar ta Masar ta fada cikin rudanin siyasa tun lokacin da sojoji suka kifar da gwamnati Mohamed Mursi a farkon watan Yuli. Kuma yanzu hukumomin kasar sun dauki tsauraran matakai kan magoya bayan 'yan kungiyar ta 'yan uwa Musulmai, saboda saka ta a matsayin ta 'yan ta'adda, abin da ya bakanta ran magoya bayan kungiyar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh