Rikicin Libya na son tallafin kasa da kasa | Labarai | DW | 17.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Libya na son tallafin kasa da kasa

Masar ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya shiga tsakani a rikicin kasar Libya a daidai lokacin da mayakan IS ke cin karansu babu babbaka a wasu yankunan kasar.

Shugaba Abdel-Fattah al-Sissi na kasar ta Masar a ranar Talatan nan ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya shiga tsakani kan rikicin da ke faruwa a kasar Libya, kwanaki biyu bayan da mayakan IS suka fitar da wani bidiyo da ke nuna yadda suka yanka wasu mabiya addinin Kirista 'yan asalin kasar ta Masar guda 21.

A cewar shugaba al-Sisi akwai bukatar samun goyon baya wajen shigar al'ummar kasar ta Masar da ma gwamnatin kasar kan duk wani yunkuri na shiga tsakanin.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi a zantawarsa da gidan rediyon Europe 1 na kasar Faransa bayan da dakarun sojan sama na kasar ta Masar suka yi lugudan wuta a kan mayakan na IS kwana guda da ya gabata.

Shi kuwa jakadan Majalisar Dinkin Duniya Bernardino Leon da ke sanya idanu kan ayyukan hukumar a kasar ta Libya, ya bayyana cewa akwai tanade-tanade da ake da su a kasa muddin shirin samar da sulhu a tsakanin bangarori masu adawa da juna ya gaza nasara.