1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Libiya ya na shafan man fetur

Suleiman BabayoMarch 3, 2015

Jirgin yaki ya kai farmaki a an tasoshin jiragen ruwa da ake dakon man fetur na Libiya da su. Tun shekaru hudun da suka gabata Libiya ke Fama da rikicin siyasa.

https://p.dw.com/p/1EkID
Libyen Sirte Unruhen IS
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. B. Khalifa

Jirgin saman yaki mallakin dakarun kasar Libiya wanda ya ke sintiri a birnin Tripoli fadar gwamnatin kasar ya yi barin wuta a wasu tashoshin jiragen ruwa biyu da ake dakon man fetur, abin da ya haifar da takaitaccen ta'adi.

Wuraren hakar man fetur sun kasance inda ake kai wa hare-hare tun lokacin da rashin jituwa ke karuwa tsakanin bangarori biyu da ke ikirarin mulkin kasar. Yanzu haka kasar ta na iya fitar da gangunan danyen man fetur 400,000 a kowace rana, maimakin miliyan daya da dubu-dari-shida da take fitarwa kafin rikicin ya barke kimanin shekaru hudu da suka gabata.

Gwamnatin da ke samun goyon bayan kasashen duniya ta rantsar Janar Khalifa Haftar wanda yake yaki da masu kaifin kishin addinin Islama, a matsayin babban hansan soji. Kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka ta fada rudanin siyasa da tattalin arziki a shekara ta 2011 bayan boren da ya kawo karshen gwamnatin Marigayi Mu'ammar Gaddafi.