Rikicin kudurin doka a Zimbabwe | Labarai | DW | 27.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kudurin doka a Zimbabwe

Jamiyar dake mulki a kasar Zimbabwe ta amince da wani kudurin doka da ya bukaci kwace kashi 51 cikin dari na harkokin kasuwancin fararen fata domin baiwa bakar fatar kasar.

Membobin jamiyar dake mulki a majalisar wakilai sun amince kann kudurin dokatar da a cewarsu zata habaka tattalin arzikin bakar fatar kasar.Sai dai membobin jamyiun adawa sun fice daga zauren majalisar suna masu cewa dokar tana nuna bambamcin launin fata kuma bata bisa tsarin mulkin kasar.

Kodayake ana jiran amincewar majalisar dattaijai wadda jamiyar dake mulki take da rinjaye ciki kafin a mika dokar gaban Mugabe wanda ya kirkiro da ita domin ya sanya hannu akai.