Rikicin kasar Iraki | Labarai | DW | 18.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kasar Iraki

Fiye da mutane 70 suka rigamu gidan gaskiya a jerin tashe tashen hankula da suka wakana yau talata a fadin kasar Iraqi. Hari mafi muni kuwa an kai ne akan garin Kufa na mabiya darikar shi´a, inda wani dan kunar bakin wake ya halaka mutane kusan 60. Dan kunar bakin wake dai ya tuka wata karamar safa ce zuwa gaban wani masallaci, inda wasu leburori ke jiran a dauke su aiki. A can garin Hawiya na ´yan suni dake arewacinIraqi mutane akalla 8 sun rasu a wani harin bam da aka kai kan wata motar ´yan sanda dake sintiri. Sannan a Basra dake kudancin kasar mutum 5 dukkan su magoya bayan

malamin ´yan shi´a mai matsanancin ra´ayi Moqtada al-Sadr sun rasu a wata musayar wuta da suka yi da sojojin Birtaniya.