Rikicin Kamaru: Sarakunan gargajiya na tserewa zuwa tudun mun tsira | Siyasa | DW | 21.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin Kamaru: Sarakunan gargajiya na tserewa zuwa tudun mun tsira

Sarakunan gargajiya da dama sun gudu daga fadar mulkinsu a yankin da ke magana da harshen Ingilishi na Kamaru bayan kisa wani Basarake.

Taron shugannin al'umma a Kamaru na mika makamai a maye gurbinsu da kekuna

Taron shugannin al'umma a Kamaru na mika makamai a maye gurbinsu da kekuna

Bayan da wasu mutane dauke da makamai suka kai hari a wata majami'a inda suka hallaka sarkin gargajiya na kabilar Afos, wasu sarakunan gargajiya sun tsere daga fadar mulkinsu a yankin da ke magana da harshen Ingilishi na kasar Kamaru, da ke fama da rikici.

A watan da ya gabata ma dai, an sace wasu sarakunan gargajiya takwas a yankin tare da yin garkuwa da su, kafin daga bisani suka hallaka guda daga cikinsu, bisa zargin da 'yan bindigar suka yi musu na hada baki da gwamnati domin a yaki 'yan aware.

Wadannan maharan dai sun saki ragowar sarakunan bakwai, bayan da suka sha suka. Sarakunan sun tsere inda suka bayyana cewa sun dauki matakin guduwa ne saboda tsoron abin da ka je ya zo. Mutane da dama sun taru a cocin Katolika da ke garin Buea a yankin Kudu maso Yammacin kasar ta Kamaru, domin yin addu'a ga marigayi sarkin gargajiyar Balondos Cif Itoh Esoh Stephen da 'yan bindigar suka kama a cocin Ekondon Titi tare da hallaka shi. Daga cikin wadanda suka halarci taron addu'ar ga marigayin akwai 'yarsa Panjie Itoh wadda cikin kuka ta ce da mahaifinsu ya sauraresu da bai mutu ba.

'''Ya'ya da iyalai sun roke shi ya gudu saboda ana ta yi masa barazana, sai dai ya ce yana yi wa al'ummarsa aiki. In har zai mutu to zai mutu da al'ummarsa. A karshe ya mutu a dakin Allah, a matsayinsa na mutumin da ke son Allah. Sai dai na tabbata Allah ne ya hukunta cewa ta wannan hanyar zai mutu. Allah ya san dalili."

An girke dubannen dakarun tsaron Kamaru a yankunan masu magana da Ingilishi

An girke dubannen dakarun tsaron Kamaru a yankunan masu magana da Ingilishi

Cif Ebong Joseph na kauyen Atati a yankin na Kudu maso Yammacin kasar ta Kamaru ya samu nasarar tserewa zuwa Najeriya. A wata hira ta wayar tarho, ya bayyana cewar ba zai koma Kamaru ba har sai an samu zaman lafiya a yankin da ke magana da harshen Ingilishi na kasar. Ya yi kira ga gwamnatin kasar da kuma al'ummomin kasa da kasa da su kawo dauki domin ganin yadda za a shawo kan rikicin da kasar ke fama da shi wanda ke neman rikidewa zuwa yakin basasa.

A nasa bangaren, gwamnan Kudu maso Yammacin Kamaru, Bernard Okalia Bilai ya yi kira ga sarakunan da su koma masarautunsu, inda ya ce an tura sojoji domin kare lafiyarsu da ta al'ummarsu yana mai cewa.

"Ya kamata su dawo gidajensu. Jami'an tsaro na nan za su ba su kariya daga aikin 'yan ta'adda. Muna yin kira ga sarakunan gargajiyar su dawo."

'Yan awaren da ke tayar da kayar bayan dai, ba su taba musanta cewa ba sune ke da alhakin sacewa tare da hallaka sarakunan ba, akasin haka ma gargadi suka yi ga sarakunan a shafukan sada zumunta na zamani, kan hada baki da gwamnati. A hannu guda gwamnatin na cewa ta dora alhakin kawo karshen yakin da yankin masu magana da harshen Ingilishin na Kamaru ke fama da shi a kan sarakunan, tun da ana ba su albashi domin kula da al'umma.

Sauti da bidiyo akan labarin