Rikicin Ghouta ya hallaka fararen hula 500 | Labarai | DW | 24.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Ghouta ya hallaka fararen hula 500

Barin wutar da dakarun gwamnatin Siriya ke yi a Ghouta da ke wajen birnin Damuscus ya yi sanadin rasuwar mutane kimanin dari biyar a kwanakin 7 da suka gabata.

Daga cikin wannan adadi 121 yara ne kanana kamar yadda hukumar nan da ke sanya idanu kan sha'anin kare hakkin dan Adam ta Siriya wato Syrian Observatory for Human Rights ta shaida a wannan Asabar din sai dai ya zuwa yanzu ba wata kafa mai zaman kanta da tabbatra da hakan.

Wannan na zuwa ne bayan da jami'an diflomasiyya na kasashe daban-daban da ke zauren Majalisar Dinkin Duniya suka amince da kada kuri'ar s gobe Lahadi don ganin an samu tsagaita wuta a rikicin na Siriya. Wannan tsagaita wuta inji masu ruwa da tsaki kan yunkurin wanzar da zaman lafiya a kasar wata kafa ce ta samar hanyar shigar da kayan abinci da magunguna ga wadanda ke bukata kana za ta bada dama ta fidda fararen hula daga wajen da ake gwabza fada tsakanin 'yan tawaye da sojin gwamnati.