1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a ofishin jakadancin Koriya ta Kudu

June 16, 2020

Ma'aikatar tsaro ta Koriya ta Kudu ta fitar da wani bidiyo a wannan Talata da ke nuna wani abun fashewa da ya tarwatse a ofishin jakadancin kasar da Koriya ta Arewa.

https://p.dw.com/p/3drS0
Nordkorea Kim Jong-un
Hoto: picture-alliance/AP/Korea News Service/Korean Central News Agency

Abin dai ya tarwatse ne a ofsihin jakadancin kasashen biyu da ke garin kan iyaka na Kaesong.  Hotunan bidiyo da aka wallafa sun nuna yadda wani bakin hayaki ya rinka fitowa daga wannan ofishi. 

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce harin ya sa ana zargin gwamnatin Koriya ta Arewa da kokarin tayar da hankalin kasashen biyu, a kokarin da take yi na mayar da martani a akan wasu takardun cin mutunci da ake yadawa game da shugabanta Kim Jong Un.