1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Shirin rantsar da shugaban kasa

Rahmatu Abubakar Mahmud LMJ
January 7, 2021

Jami'an tsaro sun yi amfani da karfin tuwo wajen tabbatar da doka da oda a harabar majalisar dokokin kasar Ghana, biyo bayan wani hargitsi tsakanin 'yan adawa da na masu rinjaye.

https://p.dw.com/p/3ndgF
Ghana Präsident Nana Addo Dankwa Akufo-Addo
Shugaba Nana Akufo-Addo na Ghana zai sake shiga fadar shugaban kasaHoto: Anthony Anex/KEYSTONE/picture alliance

Masu aiko da rahotanni sun ce rikicin ya barke ne a daidai lokacin da 'yan majalisar ke tsaka da zaben kakakin majalisar dokoki, bayan da wani dan majalisar daga bangaren jam'iyya mai mulki ya rungumi akwatin kuri'un zaben. Nan take dai hayani ta barke, inda bangaren jam'iyyar adawa ya zarge shi da niyar aikata magudi.

Karin Bayani: Sharhi kan zaben Ghana na 2020

Tun bayan kammala zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin da bangaren adawa da na masu mulki suka yi kan-kan-kan ne dai, ake ta fuskantar takun saka tsakanin bangarorin biyu a kasar Ghana, kasar da daukacin kasashen yammacin Afirka ke kallo abar misali a fannin dimukuradiyya.

Karin Bayani: Zaben Ghana na 2020

Bayan kammala zaben shugaban Majalisar dokokin dai, za a rantsar da shugaba mai ci Nana Akufo-Addo a karo na biyu a karo na biyu, bayan da ya lashe zaben da jagoran adawa kana tsohon shugaban kasar ta Ghana John Dramani Mahama ya yi zargin an tabka magudi.