Rikici tsakanin tsagerun Libiya | Labarai | DW | 08.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici tsakanin tsagerun Libiya

Mutum guda ya mutu wasu sun samu raunika a rikicin da ya barke a Libiya

Akalla mutum daya ya mutu wasu 10 sun samu raunika, sakamakon kwashe tsawon lokaci ana fafatawa tsakanin kungiyayin tsagerun kasar Libiya biyu masu dauke da makamai.

Shaidun gani da ido da hukumomi sun ce, lamarin da ya faru a wannan Alhamis da ta gabata, ya kai ga amfani da muggan makamai tsakanin sassan biyu a Tripoli babban birnin kasar. Wasu majiyoyi sun ce, wasu gungun tsageru daga birnin Misrata suka kai harin ramuwar kisan mutanensu a birnin na Tripoli, abin da ya haddasa fadan na jiya ke nan.

Kasar ta fada cikin rudani tun bayan kifar da gwamnatin Marigayi Mu'ammar Gaddafi cikin shekaru biyu da suka gabata, da taimakon kungiyar tsaro ta NATO-OTAN. Kuma tun wannan lokaci man fetur da take fitarwa zuwa kasashen ketere ya yi matukar raguwa, saboda yadda tashe-tashen hankula suka kassara kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu