Rikici na kara tsananta a Kamaru | Siyasa | DW | 23.01.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikici na kara tsananta a Kamaru

Gwabza wa tsakanin 'yan awaren yankin Kamaru a yankin kasar mai magana da Turancin Ingilishi, ya kai ga mutuwar mutane shida, yayin da gungu daya ya yi garkuwa da fiye da mutane 35 na daya bangaren.

Sojojin Kamaru na sintiri yayin rikicin yankin 'yan Awaren kasar

Sojojin Kamaru na sintiri yayin rikicin yankin 'yan Awaren kasar

Shugabannin 'yan awaren sun daura alhakin abin da ke faruwa, da kutsen da aka yi musu daga bangaren sojojin gwamnati, amma tuni sojojin suka musanta hakan. Wani wanda ake kiran kansa da Janar Chacha, mayaki na bangaren 'yan awaren, masu magana da Turancin Ingilishi a yankin arewa maso yammacin Kamaru, a cikin wani sakon da aka yada a kofofin sada zumunta na zamani ya ce matakansa na yakin neman cin gashin kan kudancin Kamaru, shi ne tabbatar da samun 'yanci:

"Abin da nake fada shi ne ba za mu taba zagon kasa ga wannan fada ba. Idan ka yi zagon kasa, Ni Chacha zan neme ka har sai na same ka. Gwamnatin kasa ta neme ni, amma ba ta yi nasara ba. Ina nan ban kuma tsere ba. Ina fada."

Gawar mutane biyu da aka kashe a rikicin

Gawar mutane biyu da aka kashe a rikicin

A farkon mako aka fito da wannan faifan magana da aka nada, kwana guda bayan wasu da ke biyayya ga shi mayakin Chacha, sun nuna hotunan kimanin mutane 40, da suka ce na bangaren wasu mayaka ne, da suka fandare. Shida daga cikin na bangaren Efang ne, inda aka samu gawar wani Janar, na wani gungun 'yan awaren daga bisani.

Tapang Ivo Tanku da ke kasar Amirka mai magana da yawun kungiyar tsaron bangaren yankin Kamaru mai magana da Turancin Ingilishi, wanda yake da zama a kasar Amirka ya ce wanda aka kashe da wadanda aka kama suna daga bangaren da yake ne:

"Sojojin da aka kashe tun farko, Chacha ya yi garkuwa da su, wannan laifin yaki ne, da laifi ga cin zarafin bil Adama, gami da saba yarjejeniyar yaki ta birnin Geneva, kuma irin wannan abu gwamnatin Kamaru mai makwabtaka ke fatan, Ambazoniya ta kasance a ciki. Haka ya saba yarjejeniyar mutunta fursunonin yaki da birnin Geneva."

Yayin da ake kwashe gawawwakin wadanda suka mutu

Yayin da ake kwashe gawawwakin wadanda suka mutu

Sannan Tanu yana zargin sojojin gwamnatin Kamaru da raba kan 'yan awaren, na yankin mai magana da Turancin Ingilishi. Brig Janar Valere Nka kwamandan sojojin Kamaru da ke jagorancin yaki, a yankin 'yan awaren, wanda ya ce sojojin suna aiki bisa tsari da dokoki, kuma ba sa bukatar raba kan kowa. Sannan ya ce za su murkushe mayakan 'yan awaren ko kuma su mika wuya:

"Ina son mika gagarumin gargadi ga wanda yake kiran kansa Janar Chacha na karya, Mun san maboyarsu. Za mu karfafa farmakin soja idan ba su mika makamai ba, za mu murkushe su."

Fadan na kara jefa fararen hula cikin rudanin na rashin sanin wane ne ke kai musu farmaki ko kuma wake kare su.

Sauti da bidiyo akan labarin