Rikici na ci gaba da ritsawa da Libiya | Labarai | DW | 04.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici na ci gaba da ritsawa da Libiya

Fiye da mutane 20 sun hallaka a rikicin da ya gudana a birnin Tripoli na Libiya sakamakon fada tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai.

Gwamnatin Libiya ta ce fiye da mutane 20 suka hallaka, sannan wasu fiye da 70 suka samu raunika, sakamakon dauki ba dadi tsakanin kungiyoyin tsageru masu dauke da makamai a birnin Tripoli, wadanda suka kwashe mawaonni biyu suna neman karbe ikon filin jiragen sama.

Rikicin ya janyo kasashe da yawa janye jakadu daga kasar ta Libiya, yayin da gwamnati ta yi gargadin tabarbarewar lamuran rayuwa na jinkai. Mahukuntan Libiya na neman tabbatar da doka da oda tun shekara ta 2011 bayan kifar da gwamnatin Marigayi Mu'ammar Gaddafi. Amma tsageru masu dauke da makamai na ci gaba da kassara kasar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe