Rikici a Libanon | Labarai | DW | 04.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici a Libanon

A ƙasar Libanon dakarun gwamnati da yan takifen ƙungiyar Fatah Al-Islam na ci gaba da bata kashi.

A yau da safe wannan rikici ya ɓulla a matsugunan yan gudun hijira Palestinu na yankin Ain al Hiloueh.

A sakamkon tafo mu gamar da a kai daren jiya zuwa sahiyar yau, sojoji 3 na gwamnati da fara hulla 2, su ka rasa rayuka a wannan yanki, da ya ƙunshi yan gudun hijira dubu 45.

Wannan rikici ya faro ranar 20 ga watan da ya gabata, a mastugunan yan gudun hijira na yankin Nahr al Bared, kawo yanzu ya jawo mutuwar mutane fiye da 100.